Ishaya
1
Wahayi game da Yahuda da Urushalima wanda Ishaya ɗan Amoz ya gani a zamanin da Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya, suka yi mulkin Yahuda.
 
Al’umma mai tayarwa
Ku kasa kunne, ya sammai! Ki saurara, ya duniya!
Gama Ubangiji ya yi magana,
“Na yi renon ’ya’ya, na kuma raya su,
amma sun tayar mini.
Saniya ta san maigidanta,
jaki ya san wurin sa wa dabbobi abinci maigidansa,
amma Isra’ila ba su sani,
mutanena ba su gane ba.”
 
Kash, ya ke al’umma mai zunubi,
mutane cike da laifi,
tarin masu aikata mugunta,
’ya’yan da aka miƙa wa lalaci!
Sun yashe Ubangiji;
sun rena Mai Tsarkin nan na Isra’ila
suka juya masa baya.
 
Me ya sa za a ƙara yin muku dūka?
Me ya sa kuka nace ga yin tayarwa?
An yi wa dukan kanku rauni,
zuciyarku duk tana ciwo.
Daga tafin ƙafarku zuwa saman kanku
ba lafiya,
sai miyaku da ƙujewa
da manyan gyambuna,
ba a tsabtacce su ba ko a daure
ko shafa musu magani.
 
Ƙasarku ta zama kufai,
an ƙone biranenku da wuta;
baƙi suna ƙwace gonakinku
a idanunku,
ta zama kango kamar sa’ad da baƙi suka rushe ta.
An bar diyar Sihiyona
kamar rumfar mai ƙumu a gonar inabi,
kamar bukka a gonar kabewa,
kamar birnin da aka kewaye da yaƙi.
Da ba a ce Ubangiji Maɗaukaki
ya bar mana raguwar masu rai ba,
da mun zama kamar Sodom,
da mun zama kamar Gomorra.
 
10 Ku saurari maganar Ubangiji,
ku masu mulkin Sodom;
ku kasa kunne ga dokar Allahnmu,
ku mutanen Gomorra!
11  Ubangiji ya ce, “Yawan hadayunku,
mene ne suke a gare ni?”
Ina da isashen hadayun ƙonawa,
na raguna da na kitsen dabbobi masu ƙiba;
ba na jin daɗin
jinin bijimai da na tumaki da kuma na awaki.
12 Sa’ad da kuka zo don ku bayyana a gabana,
wa ya nemi wannan daga gare ku,
da kuke kai da kawowa a filayen gidana?
13 Ku daina kawo hadayu marasa amfani!
Turarenku abin ƙyama ne gare ni.
Ina ƙin bukukkuwanku na Sabon Wata, da na ranakun Asabbaci, da taronku na addini,
ba zan iya jure wa mugun taronku ba.
14 Bukukkuwanku na Sabon Wata da na tsarkakan ranaku
na ƙi su.
Sun zama mini kaya;
na gaji da ɗaukansu.
15 Sa’ad da kuka ɗaga hannuwanku wajen yin addu’a,
zan ɓoye fuskata daga gare ku;
ko da kun miƙa addu’o’i masu yawa,
ba zan kasa kunne ba.
 
Hannuwanku sun cika da jini!
 
16 Ku yi wanka ku kuma tsabtacce kanku.
Ku kawar da mugayen ayyukanku daga gabana;
Ku daina aikata mugunta.
17 Ku koyi yin nagarta; ku nemi adalci.
Ku ƙarfafa waɗanda aka zalunta.* Ko kuwa / ku tsawata wa masu zalunci
Ku ba wa marayu hakkinsu,
ku taimaki gwauruwa.
 
18  Ubangiji ya ce,
“Yanzu fa ku zo, bari mu dubi batun nan tare,
Ko da zunubanku sun yi ja kamar garura,
za su zama fari kamar ƙanƙara;
ko da sun yi ja kamar mulufi,
za su zama kamar ulu.
19 In kuna da niyya kuna kuma yi mini biyayya,
za ku ci abubuwa masu kyau daga ƙasar;
20 amma in kuka yi tsayayya kuka kuma yi tayarwa,
za a kashe ku da takobi.”
Ni Ubangiji na faɗa.
 
21 Dubi yadda amintacciyar birni
ta zama karuwa!
Dā ta cika da yin gaskiya;
dā masu adalci a can suke zama,
amma yanzu sai masu kisankai kaɗai!
22 Azurfarki ta zama jebu,
an gauraye ruwan inabinki mafi kyau da ruwa.
23 Masu mulkinki ’yan tawaye ne,
abokan ɓarayi;
dukansu suna ƙaunar cin hanci
suna bin kyautai.
Ba sa taɓa tsare marayu a ɗakin shari’a;
ba sa taimakon gwauruwa.
 
24 Saboda haka Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki,
Mai Iko nan na Isra’ila, ya furta,
“Kai, zan sami hutu daga maƙiyana
in kuma yi ramuwa a kan abokan gābana.
25 Zan juye hannuna a kanki;
zan wanke ke sarai
in fitar da dukan ƙazantarki.
26 Zan maido da alƙalanki kamar yadda suke a dā can,
mashawartanki kamar yadda suke da fari.
Bayan haka za a ce da ke
Birnin Masu Adalci,
Amintacciyar Birni.”
 
27 Za a fanshi Sihiyona da adalci,
masu tubanta kuma da aikin gaskiya.
28 Amma za a karye ’yan tawaye da masu zunubi,
waɗanda suka rabu da Ubangiji kuma za su hallaka.
 
29 “Za ku ji kunya saboda masujadan ƙarƙashin itatuwan oak
da kuka yi farin ciki;
za a kunyata ku saboda lambun
da kuka zaɓa.
30 Za ku zama kamar itacen oak mai busasshen ganyaye,
kamar lambu marar ruwa.
31 Mutum mai ƙarfi zai zama kamar rama,
aikinsa kuma kamar tartsatsin wuta;
duka za su ƙone tare,
ba kuwa wanda zai kashe wutar.”

*1:17 Ko kuwa / ku tsawata wa masu zalunci