Yowel
1
Maganar Ubangiji wadda ta zo wurin Yowel ɗan Fetuwel.
 
Mamayar da fāra ta yi
Ku ji wannan, ku dattawa,
ku kasa kunne, dukan waɗanda suke zaune a ƙasar.
Ko wani abu makamancin haka ya taɓa faruwa a kwanakinku
ko a kwanakin kakanninku?
Ku faɗa wa ’ya’yanku,
bari kuma ’ya’yanku su faɗa wa ’ya’yansu,
’ya’yansu kuma su faɗa wa tsara ta gaba.
Abin da ɗango ya bari
fāri masu girma sun cinye;
abin da fāri masu girma suka bari,
burduduwa ta cinye;
abin da burduduwa ta bari sauran kwari* A nan ma’anar kalmomin nan huɗu na Ibraniyanci da aka yi amfani da su da yake nuna fāra ba a san tabbatacciyar ma’anar ba. sun cinye.
 
Ku farka, ku bugaggu, ku yi kuka!
Ku yi kuka da ƙarfi, ku dukan mashayan ruwan inabi;
ku yi kuka mai ƙarfi saboda sabon ruwan inabi,
gama an riga an ƙwace ta daga leɓunanku.
Wata al’umma ta mamaye ƙasata,
tana da ƙarfi ba ta kuma ƙidayuwa;
tana da haƙoran zaki,
da zagar zakanya.
Ta mayar da kuringar inabina kango
ta kuma lalatar da itatuwan ɓaurena.
Ta ɓamɓare bayansu duka
ta kuma jefar da su
ta bar rassansu fari fat.
 
Ku yi makoki kamar budurwa Ko kuwa yarinya
a cikin tsummoki
tana baƙin ciki domin mijinta Ko kuwa wanda suka yi alkawarin aure na ƙuruciyarta.
Hadayun hatsi da hadayun sha
an yanke su daga gidan Ubangiji.
Firistoci suna makoki,
su waɗanda suke yi wa Ubangiji hidima.
10 Filaye sun zama marasa amfani,
ƙasa ta bushe;§ Ko kuwa ƙasa tana makoki
an lalatar da hatsi,
sabon ruwan inabin ya bushe,
mai kuma ba amfani.
 
11 Ku fid da zuciya, ku manoma,
ku yi ihu, ku masu noma inabi;
ku yi baƙin ciki saboda alkama da sha’ir,
saboda an lalata girbin filaye.
12 Kuringar inabin ta bushe
itacen ɓaure kuma ya yi yaushi,
’ya’yan rumman, itacen dabino da itacen gawasa,
dukan itatuwan filaye, sun bushe.
Tabbatacce farin cikin ’yan adam
ya bushe.
Kira don makoki
13 Ku sa tsummoki, ya firistoci, ku yi makoki;
ku yi ihu, ku da kuke yin hidima a gaban bagade.
Zo, ku kwana saye da tsummoki,
ku waɗanda kuke yi wa Allahna hidima,
gama an yanke hadayun hatsi da hadayun sha
daga gidan Allahnku.
14 Ku yi shelar azumi mai tsarki;
ku kira tsarkakan taro.
Ku kira dattawa
da kuma dukan mazaunan ƙasar
zuwa gidan Ubangiji Allahnku,
ku kuma yi kuka ga Ubangiji.
 
15 Kaito saboda wannan rana!
Gama ranar Ubangiji ta kusa,
za tă zo kamar hallaka daga wurin Maɗaukaki.* Da Ibraniyanci Shaddai
 
16 Ba a yanke abinci
a idanunmu,
farin ciki da kuma murna
daga gidan Allahnmu ba?
17 Iri suna ta yanƙwanewa
a busasshiyar ƙasa ma’anar wannan kalma da Ibraniyanci ba ta da tabbas.
Ɗakunan ajiya sun lalace,
an rurrushe rumbunan hatsin,
gama hatsi ya ƙare.
18 Ji yadda dabbobi suke nishi!
Garkunan shanu sun ruɗe
saboda ba su da ciyawa,
har garkunan tumaki ma suna shan wahala.
 
19 A gare ka, ya Ubangiji, nake kira,
gama wuta ta cinye wurin kiwo
harshen wuta kuma ya ƙone dukan itatuwan jeji.
20 Har ma namun jeji suna haki gare ka;
rafuffuka sun bushe
wuta kuma ta cinye wurin kiwo a jeji.

*1:4 A nan ma’anar kalmomin nan huɗu na Ibraniyanci da aka yi amfani da su da yake nuna fāra ba a san tabbatacciyar ma’anar ba.

1:8 Ko kuwa yarinya

1:8 Ko kuwa wanda suka yi alkawarin aure

§1:10 Ko kuwa ƙasa tana makoki

*1:15 Da Ibraniyanci Shaddai

1:17 ma’anar wannan kalma da Ibraniyanci ba ta da tabbas.