×
Home: Mobile Home: Original Style Christian Netflix Jewish Stories X-Witch X-Muslim MP3 Bible Bible Movies Gospel Videos Godly Movies CBN Videos Kids Videos Worship Music Vids for New Believers Random Video What's New
  Kat Kerr   Anna Rountree   Mary Baxter   Several #1   Several #2   Choo Thomas   Ian McCormack   Burpo   I saw His Glory   7 Colombian Youths   Heavenly Blood   Heaven Testimonies
  Lazarus   Bill Wiese   Mary Baxter   Dr. Rawlings   J. Perez   Hepzibah   Ptr. Park   7 Columbian Youths
  Atomic Prayer   Prayers that ROUT demons   Warfare + Blessing   Healing   Declaration   101 Decrees   Tongues   Rosary   Artic Fire   Why Should We Pray?   Why Bother
  MP3 Bible   10 Commandments   Learn Bible in 24 Hours   40 Spiritual Lessons   Alpha   Foundations   Bible Commentaries   Book of Mormon   Temple Study   Red Letters   Divine Healing Training   God Story   Gap Theory   Creation to Christ   Book of John   Kids Bible Cartoons   Derek Prince Teaching   Jesus Film   Digital Bible   Bible Codes ELS
  Passion of Christ   New Jesus Film   Introduction   Names of God   Jesus IS...   Jesus Film   That's My KING   Father's Love Letter   Celestial Hug
  Warfare Training 1   Warfare Training 2   Casting Out demons   Combat   Examples   Warrior King   Exorcism   Prayer   Ask Him   demonology   Clarita   NUWI
  Final Quest   The Call   Tommy Hicks   3 Days   Angel Song   The Prison   H.A.Baker
  Best #1   Best #2   Spiritual Food   Generals   Ramirez   Bishop Kelley   Gary Wood   Roland Buck   Rees Howells   Baptized by Fire   Sid Roth   Todd White   Gary Beaton   Victor Marx   Akiane   Theo Nez   Nun's Story   Retha McPherson   Tomas Welch
  Booth's Vision   Frank Jenner   Hell's Best Kept Secret   EE-Taow   Manifesting Power   LivingWaters   Atheist Delusion   Using AI for Jesus   Sharing w/ Muslims   Sword + Serpent
  Revival Hymn   Jesus in China   Freemason Curruption   Modern Child Sacrifice   the WAR on Children   XGay   Transformations   Ark of Covenant   Soul Ties   Last Reformation   Noah's Ark Found   Does GOD Exist   Political Issues   Fake Mountain   7 Mountains   ID vs Evolution   Bible Science   American History   China Records   Case: Creator   Case: Christ   Case: Faith   Little Lessons   Deadly Mistakes   Enemies Within   Chinese Characters   Global Warming   The Final Frontier   Understanding Israel   Testing Joseph Smith   Targeting Kids
  X-Muslim   Journey of Hope   Islam Rising   ACT   Jihad   Best Muslim Story   Enemies Within   Answering Islam   Killing for Heaven   Killing the Infidel
  Downloadable MP3 Worship Music   Online Worship Music  DivineRevelations University   Free Posters   Christian Pictures   Kids Christian Cartoons   Bible Trivia   End Times Visions   Fractal Praise   Communion Verses   Bobby Conner   Brother Yun   Civil War   Prayer Tank   Fiscal Cliff   Understanding Economics   Who takes the Son   Christian GPTs
  All Languages   Afrikaans   Albanian   Amharic   Arabic   Bengali   Bulgarian   Burmese   Cambodian   Catalan   Chinese   Czech   Danish   Dutch   Farsi   Finnish   French   German   Greek   Gujarati   Hausa   Heberw   Hindi   Hungarian   Indonesian   Italian   Japan   Kannada   Khazanah   Korean   Laos   Malagasy   Malayalam   Malaysian   Marathi   Mongolian   Nepali   Norwegian   Oriya   Polish   Portuguese   Punjabi   Romanian   Russian   Somali   Samoan   Serbo_Croatian   Sinhala   Slovak   Slovenian   Spanish   Swahili   Swedish   Tagalog   Tamil   Telugu   Thai   Tongan   Turkish   Ukrainian   Urdu   Uzbek   Vietnamese
 About  Disclaimer  Phone# USA 425-610-9216  [email protected]
Follow on YOUTUBE  YouTube Follow on Facebook  Facebook Follow on X/Twitter  X/Twitter Follow Podcast RSS  Podcast  RSS Follow on Instagram  Instagram Follow on TikTok  TikTok
  PDF Library   Believer's Authority   Heavenly Man, Yun   Torch + Sword   The Harvest   Faith Shoemaker's Vision   Daughter of Sacrifice
AI Tech Site Something Funny... 2nd Page, Older Material
×


Menu / Home
Menu / Home

HTML Bible Gospel Go The Prophet's Story Passion of the Christ The Jesus Film 4 Spiritual Laws
Ruya Game Da Aljanna     WAHAYI AKAN JAHANNAMA     Muslim Dreams/Mohammed  MP4 Hi Low      LOKACI NA WUCEWA DA SAURI

--- (Shaida na farko, Esau) ---

2 Korinthiyawa 12:2

Na san wani mutum chikin Kristi, yau shekara goma sha hudu ne (ko chikin jiki ne, ko ba tare da jiki ba, ban sani ba; Allah Ya sani), wannan mutum dai an fyauche shi har sama ta uku.

HeavenA farko dai muna cikin daki ne, sai hasken bayanuwar Ubangiji ta cika dakin wadda ya haskaka dukan dakin. Dakin  ya cika da daukakar Ubangiji, abu mai kyau ne ka zama a gaban Ubangiji.

Yesu Ya ce mana “’ya’yana zan nuna maku mulki Na, zamu je wajen daukakata.” Sai muka rike hannayen junan mu, sai aka daga mu zuwa sama, da na kalli kasa, sai na ga ba’a cikin wannan jiki muke tafiya ba, nagan jikinamu a kasa. Da muka bar wannan jiki, an sa mana dogayen kaya sai mu ka fara tafiya sama da gudu.

Mun isa gabar wasu kofofi wadda hanya ne zuwa mulkin sama. Mun yi mamakin abin da ke faru da mu. Abin godiya shi ne Yesu dan Allah na tare da mu, tare da mala’iku guda biyu, kowannen su  na da fukafuki guda hudu.

Mala’ikun su ka fara yin mana magana amma bamu fahimce su ba. Yarensu daban ne da namu, ba kuwa kamar yaren duniyan nan ba ne.  Mala’ikun  su ka marabce mu suka bude mana kofofin. Wannan wurin abin alajibi ne da abubuwa daban-daban. Da muka shiga ciki sai salama ta cika zukatar mu. Littafi Mai Tsarki ta ce Allah zai bamu salama wadda zata cika zukatan mu a cikin Yesu (Filibbiyawa 4:7)

Abinda na fara gani barewa ce, sai na  tambayi abokiya ta “Sandra, ki na ganin abinda na ke gani?” Ba ta kuka ko ihu kamar a lokacin da aka nuna mana jahannama, ta na murmushi, sai ta ce “I Esau, ina ganin barewar!” A nan ne na san cewa duk abubuwan da ke faruwa da gaskiya ne, cikin mulkin sama mu ke. Mun manta duk abubuwan da muka gani a jahannama. Muna jin dadin mulkin Ubangiji. Sai muka je wajen da barewar ta ke, a bayan ta akwai wata babbar itace wadda take tsakiyar aljanna.

Littafi Mai Tsarki ya gaya mana a cikin Ruya ta Yohanna 2:7 “Wanda ya keda kunne, bari shi ji abinda Ruhu ke fadi ma ekklesiyai. Wanda ya yi nasara, a gareshi zan bayas da chi daga chikin itace na rai, wanda ke cikin paradise na Allah”

Itacen ta na kwatanchin Yesu domin shi ne rai na har abada. Bayan wannan itacen akwai wata kogi wadda ruwar tana da kyau da kuma haske, wadda ba mu taba gani a duniya ba.

Kamar mu yi ta zama a wannan wajen. Sau dayawa  sai mu ce wa Ubangiji “ muna  rokon Ka ya Ubangiji kar ka dauke mu daga wannan wajen, muna so mu zauna a nan har abada! Ba mu so mu koma duniya kuma!” Sai Ubangiji ya amsa mana Ya ce “Ya kamata ku koma domin ku shaida duk abinda na shirya wa masu kauna ta domin Ina dawowa, in ba wa kowa sakamakon aikin sa”.

Da muka ga wannan kogin sai muka gudu muka fadi a ciki, mun tuna inda maganar Allah ya ce – wanda yana bada gaskiya gareni, kamar yadda nassin ya fadi, daga chikin chikinsa koruna na ruwa mai-rai za su gudu (Yohanna 7:38). Kamar akwai rai a cikin ruwar wannan kogin domin da muka shiga cikin ruwan muna iya numfashi kamar a waje mu ke. Wannan kogin na da zurfi kwarai, akwai kuma kifaye masu launi daban-daban suna yawo a ciki. Haske da ke cikin ruwan da wanda ya ke waje duk daya ne, domin a sama babu takamammen abu daya da ke bada haske, kome na da haske. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Ubanguji Yesu shi ne hasken wannan birnin (Ruya ta Yohanna 21:23). Da hannayen mu, muka kama kifi a cikin ruwan, amma ba su mutuba. Sai muka gudu zuwa wajen Ubangiji muka tambaye dalili, sai Ubangiji ya yi murmushi Ya amsa ya ce a sama babu mutuwa, babu kuka, babu kuwa azaba (Ruya ta Yohanna 21:4).

Da muka fita daga cikin ruwan mun zagaya zuwa duk inda zamu iya zuwa, muna so mu taba, mu kuma ga kome. Muna so mu dauki kome mu dawo gida da su domin suna ba mu mamaki. Babu kalmomin da za su bayana yadda sama ta ke. A lokacin da manzo Bulus ya je sama, bai iya bayana abubuwan da ya gani ba domin abubuwan alajibi da ya gani kalmomi ba za su iya kwatantawa ba. (II Korinthiyawa 12).  Akwai abubuwan da muka gani da ba zamu iya kwatantawa ba.

Daga nan muka je wata gabjejen wuri, wurin na da kyau da kuma ban mamaki. Wajen na cike da duwatsu masu tamani kamar su zinariya, emeralds, rubbies da lu’ulu’u. Kasan wajen an yi sa ne da zinari. Sai mu ka  je wani wuri inda akwai manya –manyan littattafai guda uku. Littafi na farko Littafi Mai Tsarki ne wadda aka yi sa da zinari. A littafin Zabura an gaya mana cewa Maganar Allah har abada ne zai kuwa zauna a sama har abada. (Zabura 119:89) Kowanne shafi, da rubutu da dukan abinda ke wannan babban littafi Mai Tsarkin an yi sa ne da zinariya.

Littafi na biyu da muka gani ya fi Littafi Mai Tsarkin girma, ya na bude, wanni mala’ika yana zaune yana rubutu a cikin littafin. Tare da Ubangiji Yesu muka je kusa domin mu ga abinda mala’ikan ke rubutawa. Mala’ikan na rubuta dukan abubuwan da ke faruwa a duniya. Duk abin da ya taba faruwa, da ranar, da sa’ar an rubuta su duka a wannan littafin. An yi wannan domin maganar Ubangiji ta cika inda ya ce an bude littattafan, an kuma sharanta mutanen duniya gwalgwadon ayyukan su da aka rubuta cikin littattafan (Ruya ta Yohanna 20:12). Mala’ikan ya na rubuta duk abubuwan da mutane ke yi a duniya, ko kyakkyawa ko mumuna.

Mun je wajen littafi na ukun, shi kuma ya fi sauran girma. Littafin na rufe amma mun je kusa da shi. Ubangiji ya umurce mu, mu bakwai mu saukar da littafin daga inda ya ke ajiye muka daura a kan ginshiki

Ginshikai na sama abun ban mamaki ne! Ba a yi su kamar na duniya ba, ginshikain su na nan kamar kiso ne wadda anyi su da duwatsu masu tamani, sauran an yi su da duwatsu daban-daban. Sai na gane cewa lallai Allah ne mai abu duka, kamar yadda aka rubuta a cikin littafin Haggai 2:8 cewa “zinari da azurfa duk nawa ne”. Na gane cewa Allah na rike da duk arzikin duniya, na kuma gane cewa duniya da duk abinda ke cikinta na Ubangiji ne, zai kuwa ba wa duk wadda ya tambaye shi cikin bangaskiya.

Ubangiji ya ce (Zabura 2:8) “Ka yi roko, zan kuwa ba ka dukan al’ummai, Dukan duniya kuma za ta zama taka”. Wannan littafin da muka daura a kan ginshiki yana da girma sosai, wadda karfin mu bude kowanne shafiba sai mun yi tafiya daga gefe daya zuwa karshen littafin. Mun yi kokari mu karanta abin da ke rubuce a cikin littafin kamar yadda Ubangiji Ya umurce mu. A farko dai ba mu iya karantawa ba domin an rubuta ne a cikin wata yare daban da kowanne yare na duniya, yaren sama ne. Amma  da taimakon Ruhu Mai Tsarki, an bamu alherin fahimta. Ya faru kamar an cire mana abin da ke rufe mana ido, sai mun gane rubutun, kamar yaren mu muke karantawa.

Mun ga sunayen mu a rubuce a wannan littafin. Ubangiji ya gaya mana cewa wannan ita ce littafin rai (Ruya ta Yohanna 3:5). Mun lura cewa sunayen mu da aka rubuta a cikin wannan littafin daban ne da wadanda ake kiran mu a duniya; wadan nan sabobin sunaye ne, domin  maganar Ubangiji ta cika wadda ya ce zai ba mu sabin sunaye wadda ba mai saninsa sai shi wanda ya karba (Ruya ta Yohanna 2:17)

Da muke sama, mun iya kiran wadannan sunayen na mu amma da Ubangiji ya dawo da mu duniya, an cire su daga tunanin mu, daga kuma zukatar mu. Maganar Allah har abada ne kuma dole ne ya cika. Abokina littafi Mai Tsarki ya ce (Ruya ta Yohanna 3:11) kada ka bar kowa shi amshi rawaninka ko ya cire ka daga wannan waje wadda Uba ya shirya maka. A sama akwai dubban abubuwan ban mamaki da ba za mu iya fadi da bakin mu ba. Amma ina so in gaya maka wani abu, “Allah na jiran ka!” Kodashike sai wanda ya jimre har matuka, shi ne za ya tsira (Markus 13:13)


….(Shaida na biyu, Ariel)….

Da muka fara tafiya zuwa  mulkin sama, mun isa wata kyakkyawar waje mai kofofi masu tamani. A gaban kofofin akwai mala’iku guda biyu. Sun fara magana, amma maganar su ta mala’iku ne mu kuwa ba mu fahimci abinda suke fadi ba. Amma Ruhu Mai Tsarki ya ba mu fahimta. Su na marabtar mu ne. Ubangiji Yesu ya saka hannunsa a kofofin sai suka budu. In da ba  domin Yesu na tare da mu ba, da baza mu iya shiga mulkin sama ba.

Muna ta sha’awar duk abinda muka gani a sama. Mun ga wata babbar itace wanda Littafi Mai Tsarki ya kira ta “Itace na rai” (Ruya ta Yohanna 2:7). Mun je wajen wata kogi, mun ga kifaye dayawa a ciki. Duk abubuwan na da ban mamaki, sai ni da abokai na muka shiga cikin ruwan. Sai muka fara iyo. Mun ga kifaye suna ta yawo a jikin mu. Kifayen ba su gudu kamar yadda yakan faru a duniya ba, ikon Ubangiji ya sa su sun natsu. Kifayen sun yarda da mu domin sun san baza muyi masu rauni ba. Na yi mamaki kwarai har na kama wani kifi na fitar daga ruwar amma kifin ya yi shuru yana jin dadin zama a gaban Ubangiji koda shike yana hannu na. Sai na mayar da kifin cikin ruwa.

Jesus on the white horseDaga nesa na ga akwai fararen dawakai a sama, an rubuta a maganar Allah a Ruya ta Yohanna 19:11 “Sai na ga sama a bude, ga kuma wani farin doki, da mahayansa, ana che da shi mai-aminci da mai-gaskiya; cikin adalci kwa ya ke yin shari’a da yaki kuma” Wannan dawakai su ne Ubangiji zai yi amfani da su lokacin da zai zo duniya ya dauki mutanensa, ikkilisiyar sa. Na je kusa da dawakai ina ta shafa su, sai Ubangiji ya bi ni ya kuma bar ni in hau daya daga cikin su.

Da na fara tafiya a kan dokin, sai na ji abin da ban taba jiba a duniya, sai na fara jin salama, da yanci, da kauna, da tsarki wadanda mutum zai samu a wajen nan mai kyau. Sai na fara jin dadin duk abubuwan da idanu na ke gani. Na so ne in more duk abubuwan da Allah ya shirya mana a kyakkyawar aljannan.

Mun ga tebur na bikin aure, an rigaya an shirya kome. Bashi da farko ko karshe, mun ga kujeru wadanda an shirya mana. Akwai kuma rawanin rai a shirye domin mu. Mun ga an shirya abinci masu kyau wadda an shirya wa wadanda za a gayyata zuwa bikin auren Dan Ragon.

Mala’iku su na rike da fararen yadi da Ubangiji zai yi mana riguna. Na ji mamakin ganin duk wadannan abubuwan. Maganar Allah ya gaya mana cewa dole ne mu karbi mulkin sama kamar kananan yara. (Matta 18:3) A lokacin da muke sama, muna nan kamar kananan yara, muna jin dadin kome a wajen; da furenai, da gidajen … har Ubangiji  Ya bamu izini mu shiga cikin gidajen

The banquet tableUbangiji Allah ya kai mu wanni waje wadda keda yara dayawa. Sai muka ga Ubngiji a tsakanin su, yana wasa da su. Ya dauki lokaci tare da kowannen su, Yana kuma jin dadin zama tare da su. Sai muka tambaye shi “Ubangiji wannan sune yaran da za a Haifa a duniya?” Ubangiji ya amsa ya ce “A’a wadannan yara ne da an zub da cikin su a duniya”. Da na ji haka, sai na ji jikina yayi rawa.

Na tuna da abinda na yi a shekarun baya, lokacin da ban karbi Yesu ba. A lokacin ina kawance da wata mace, har tayi ciki. Da ta gaya mani ta na da ciki, ban san abinda zan yi ba sai na ce mata ta bani lokaci in yi tunani. Lokacin da na je in gaya mata ra’ayi na, ya yi latti domin ta rigaya ta zub da cikin. Wannan ya saka mani lamba a rayuwata wadda har bayan da na karbi Yesu, na gagara in yafe wa kaina wannan abun. Amma Allah yayi wani abu ranar, Ya bar ni in shiga wannan wajen, sai ya ce mani “Ariel, ka ga wancan yarinyar? Waccan yarinyar, ‘yar ka ce” Da Ya gaya mani haka, na kalle yarinyar sai na ji ciwon da ke zuciya ta, duk wannan tsawon lokacin ya warke. Ubangiji Ya barn ni in je kusa da ita, sai na dauke ta a hannuna na kalle idanunta. Kalma daya na ji daga bakin ta “baba”, sai na fahimci cewa Allah Ya yi mani jinkai, ya kuwa yafe ni, amma ya kamata in koya in yafe kai na.

Abokina, duk wanda yake karanta wannan, ina so in gaya maka abu daya. Allah yana shirye ya yafe maka zunuban ka, yanzu kai sai ka koya ka yafe wa kanka. Ina gode wa Allah domin dammar da ya ba ni in fada maka wannan shaida. Ubangiji Yesu Kristi na ba ka yabo da daukaka. Wannan shaida ne  na Ubangiji, Ya bar mu mu ga wannan wahayi. Ina fatan cewa duk yan uwa da suka karanta wannan shaidar zasu sami albarkan wannan shaidar, su kuma albarkaci wasu da shi.

Allah Ya yi maku albarka


….(Shaida na uku)….

(Ruya taYohanna 21:4)

Za ya share dukan hawaye kuma daga idanunsa; mutuwa kwa ba za ta kara kasanchewa ba; ba kwa za a kara jin bakin zuchiya, ko kuka, ko azaba; al’amura na fari sun shude.

Da muka isa, an bude mana wannan manyan kofofin sai na ga wani kwari cike da furannai. Furannain na da kyau, kanshin su kuma da dadi. Da muka fara tafiya sai muka ji yanci da ba mu taba ji a duniya ba. Salama ta cika zuciyar mu, da mu ka kalle furen mun ga cewa daban suke, kowanne ganyen furen yana da launin sa daban.

A cikin zuciyata na ce wa Ubangiji ina son daya daga cikin wadannan furannain. Sai Ya nuna mani yardarsa. Na je kusa da furannain na ja amma ba abinda ya faru, na gagara cire fure daga kasa, na gagara cire ko ganyen. Sai Ubangiji Ya ce mani “a nan anayin kome cikin kauna” Ya taba furen, sai furen ya bada kansa ga hannun Ubangiji, Shi kuma Ya mika mana furen, sai muka cigaba tafiya da furen a hannun mu muna sunsunawa.

Mun isa wanni waje mai kofofi masu kyau. Kofofin ba kamar kowanne kofa ba ne, an yi su ne da duwatsu masu tamani. Da kofofin suka budu sai mun shiga wani daki da mutane dayawa. Kowa yana kai da kawowa, su na shirye-shirye. Wasu suna dauke da kaya  masu yalki akafadarsu, wasu suna dauke da zare na zinari, wasu kuma suna dauke da faranti mai kamar garkuwa. Dukansu suna aiki da karfinsu.

Mun tambayi Ubangiji me ya sa ake sauri haka? Sai Ubangiji Ya kira wani saurayi ya zo, wannan mutumin na rike da kaya a hannunsa. Da ban girma ya kalle Ubangiji, sai Ubangiji ya tambaye shi dalilin da yake dauke da kayan nan. Ya kalle Ubangiji ya ce “Ubangiji ka san abin da za a yi da wannan kayan! Za a yi tufafi ne na fansassu, tufafin babbar Amaryan.” Da mun ji haka, mun cika da farin ciki da salama. Ruya ta Yohanna 19:8 ya ce mana “Aka yarda mata kuma ta yafa ma kanta linen mai-labshi, mai walkiya, mai tsabta: gama adalci na tsarkaka ne”

Da muka bar wannan wajen mun ji salama domin yana da kyau ganin cewa Ubangiji da Kansa yana shirya mana abubuwa masu kyau. Yana da waje da kuma zarafi domin ka, domin  kana da muhimmanci a gare shi. Da muka fito daga wurin nan, mun cigaba da kallon kome a sama. Kamar kowanne abu a sama suna da rai kuma suna daukaka Allah.

Jesus with the ChildrenSai muka je wanni wajen da akwai dubban yara masu shekaru daban-daban. Da suka ga Ubangiji, dukansu suna so su rungume shi domin shi ne abin jin dadin su. Abin jin dadin su Yesu ne. sai mun ji kamar muyi kuka ganin yadda Ubangiji yake lura da su, ya ke sumbarsu, yake kuma rike su a hannunsa.

Munga yadda mala’iku, suke kawo wa Ubangiji jarirai a nade a cikin linen. Ubangiji yana shafa su, yana yin masu sumba, sai mala’ikun su mayar da su. Sai muka tambayi Ubangiji, me ya sa akwai yara dayawa a nan? Za a tura su duniya ne?  Tambayan  ya taba Ubangiji, sai Ya ce “A’a. Wadan nan sune wadda aka zub da cikinsu a duniya, wadanda iyayensu ba su so su haife su ba. Wadan nan ‘ya’ya na ne kuma ina kaunar su”. Na kada kai kuma muryana tayi karkarwa in tambayi Ubangiji tambaya.

A lokacin da ban san Ubangiji ba, na yi kuskure da kuma zunubi kamar kowa. Daya daga cikin wadannan zunuban shi ne wani ciki da na zubar. A lokacin na tambayi Ubangiji “Ubangiji, jaririn da na zubar waccan lokacin na nan?” Sai Ubangiji Ya ce “I”. Sai na je wani gefen da yaran suke, na ga wani kyakkyawan yaro, a kusa da shi kuma akwai mala’ika. Mala’ikan na fuskantar Ubangiji, yaron kuma ya bamu baya.

Ubangiji ya ce mani “wannan shi ne yaron ki”. Ina so in ga yaron, sai na yi gudu zuwa wajen shi, amma mala’ikan ya tare ni da hannunsa. Ya nuna mini cewa in saurari yaron. Sai na ji abinda yaron ke fadi. Yana magana yana fuskantar sauran yaran. Ya tambayi mala’ikan “baba na da mama na sun kusa zuwa ne?” Mala’ikan ya dube ni, sai ya ce “I, babanka da mamanka suna nan zuwa”.

Ban san dalilin da na sami damar jin wadan nan kalmomin ba, amma a cikin zuciyata na san wannan kalmomin babbar kyauta ce da Allah Ya ba ni. Wannan yaro yana magana ba tare da bachin rai ko bakin ciki ba domin watakila ya san bamu bari a haife shi ba, amma yana jira ne kawai da kaunar da Allah ya saka a zuciyar sa.

Mun cigaba da tafiya, amma na rike kamanin yaron a zuciyata. Na san cewa, kowanne rana zan yi kokari in ga cewa wata rana zan kasance tare da shi. Ina da wani dalili na zuwa mulkin sama, wani na jira na. Maganar  Allah ya gaya mana a cikin littafin Ishaya 65:19 “Ni kaina kuma zan cika da murna saboda Urushalima da jama’arta. Ba kuka a can, ba bukatar neman taimako”.

Mun isa wani wajen duwatsu, sai Ubangiji ya zo da rawa. A gabansa mutane ne masu yawa sake da fararen tufafi suna rike da reshen itacen zaitun. Idan sun daga rasan sama sai mai ya yi ta zubowa. Allah yana da manyan abubuwa da ya shirya maka! Yanzu ne lokacin daya kamata ka bada zuciyar ka gare shi.

Allah ya yi maku albarka


….(Shaida na hudu)….

A cikin mulkin sama mun ga abubuwan al’ajibi kamar yadda aka rubuta cikin maganar Allah a I Korantiyawa 2: 9 “Abubuwan da ido bai taba gani ba, kunne bai taba ji ba, zuciyar mutum kuma ba ta ko riya ba, wadanda Allah ya tanadar wa masu kaunarsa”.

Da muka isa mulkin sama, yana nan daban, da abubuwa manya-manya masu bada mamaki, da kuma daukakar Ubangiji. Wajen shiryayye ne, ga kuma yara dayawa. Zamu iya cewa akwai miliyan din yara a wajen.

Mun ga yara masu shekaru daban-daban, sama an raba ta zuwa kashi-kashi. Mun ga wani gidan yara mai daukar yara masu shekaru tsakanin biyu zuwa hudu (2-4). Mun gani kuma cewa a mulkin sama ma yara suna girma, akwai makarantar da ake koya masu Maganar Allah. Mallamansu mala’iku ne, suna koya wa yaran wakokin yabo, da kuma yadda za su daukaka Ubangiji Yesu.

A lokacin da Ubangiji ya iso, mun ga farin-cikin Sarkin mu. Koda shike ba mu ga fuskarsa ba, muna ganin murmushinsa. Da ya iso, duk yaran sun gudu wajensa. A tsakanin wadannan yara na ga Maryamu, uwar Ubangiji  Yesu Kristi, kyakkyawar mace ce. Ba mu gan ta a wani kursiyi ba, ba mu  kuwa ga wanni yana bauta mata ba. Ta na nan kamar sauran mata da ke sama, kamar yadda sauran mutanen duniya, ita ma ta nemi ceto ne. tana sake da fararen tufafi da bel na zinariya a kunkuminta, sumar ta kuma ta sauka har kunkuminta.

A duniya, mun ji mutane dayawa suna bauta wa Maryamu, domin ita uwar Yesu ce, amma ina so in gaya maku maganar Allah ya ce “Ni ne hanya, Ni ne gaskiya, Ni ne rai; ba mai zuwa wurin Uban sai ta wuri na” (Yohanna 14:6). Yesu ne kadai hanyar shiga mulkin sama.

Mun kuma lura cewa babu rana ko wata. Maganar Allah ya ce mana a Ruya ta Yohanna 22:5Babu sauran dare kuma; ba su kuwa da bukatar hasken fitila, ko hasken rana ba; gama Ubangiji Allah za ya ba su haske; za su yi mulki kuma har zuwa zamanun zamanai”

Yafi sauki mu bayyana wahalar da take jahannama akan mu bayyana daukakar Ubangiji, mafi wuyar ma shi ne yadda zamu bayyana halittun sama da cikawar mahallicin mu. Da muke wajen mun so mu gudu mu kalli kome da kome. Mun kwanta a ciyawa, mun ga daukakar Ubangiji. Wannan abun mamaki ne kwarai.

A sararin sama mun ga babban giciye wadda aka yi ta da zinari. Mun gaskanta cewa wannan ba bautar gumki bane amma yana nuna mana cewa ta dalilin mutuwan Yesu a kan giciye ne, muka sami shiga mulkin sama.

Mun cigaba da tafiya a sama. Abu mai dadi ne yin tafiya tare da Yesu. A can zamu san lallai wanene Allah da muke bauta wa …Yesu  banazare. Mutane dayawa a duniya sun dauka Allah na jira ne muyi zunubi domin ya horar da mu, ya tura mu zuwa jahannama amma wannan ba gaskiya ba ne. Mun ga dayan gefen Ubangiji – Yesu abokin mu ne, Yesu ya kan yi kuka a lokacin da muke kuka. Yesu Allah ne mai kauna, mai tausayi, mai jinkai kuma; Yana rike mu a hannunsa domin mu cigaba da tafiya a hanyar ceto.

Ubangiji Yesu ya bamu dammar ganin sarki Dauda, wadda aka yi maganarsa a Littafi Mai Tsarki. Kyakkyawar mutum ne, dogo, fuskar sa kuma yana nuna daukakar Ubangiji Allah. A duk lokacin da muke mulkin sama, sarki Dauda yana rawa, yana ba wa Ubangiji Allah yabo da daukaka.

Gare ku duk masu karanta wannan shaida, ina so in ce maku Maganar Allah ya ce a Ruya ta Yohanna 21:27 “ Ba kuwa wani abu mara-tsarki da za ya shiga ko kadan, ko wanda ya ke aika kazamta da karya; sai wadannan da an rubuta su a cikin littafin rai na Dan rago” . Ina so in kara fadi cewa masu karfin hali ne ke samun mulkin sama

Allah ya yi maku albarka


….(Shaida na biyar)….

(II Korantiyawa 5:10)

“Don lalle ne a gabatar da mu duka a gaban gadon shari’a na Almasihu, domin kowa ya sami sakamakon abin da ya yi tun yana tare da wannan jiki, ko mai kyau ko mara kyau.”

New JerusalemA mulkin sama mun ga sabuwar Urshalima wadda Littafi mai Tsarki ya gaya mana a Yohanna 14:2 “ A cikin gidan Ubana akwai wurin zama dayawa; da ba haka ba, da na fada maku; gama zan tafi garin in shirya maku wuri”. Mun ga wannan birni, mun kuwa shiga cikinta, birni ce mai abin alajibi! Lallai ne, Yesu ya tafi chan ya shirya mana wurin zama.

A wannan birnin mun ga gidaje dayawa, wadda akwai sunayen masu shi a gaban kowanne gida. Babu kowa a wannan birnin amma a shirye yake. An bar mu, mu shiga gidajen mu gan duk abubuwan da ke ciki. Kodashike ba mu iya tuna da abubuwan da muka gani a wannan birnin ba domin an dauke mana wannan sanin, amma mun tuna cewa ginshikan gidajen an yi su ne da karafuna masu tamani, kuma akwai duwatsu masu tamani a cikin ginshikan, suna da kuma zinari a cikin su.

Zinarin wannan birni kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya bayyana ne, za’a iya gani ta cikinsu, suna kuma yalki. Zinari da ke a duniya baza a iya kwatantasu ba da kyaun zinari da ke sama.

Bayan wannan an kai mu wani waje mai abin zuba kaya dayawa. An daskarar da hawaye ne a cikin abubuwan. Wannan hawayen kukan da ‘ya’yan Allah su ka yi a duniya. Ba hawayen guna-guni ba ne amma hawayen kukan da mutane suka yi ne a gaban Allah; hawaye na tuba, hawaye na godiya. Wannan hawaye abu mai tamani ne da Allah ya ajiye a sama, kamar yadda aka fada a Zabura 56:8 “Ka san irin wahalar da nake sha, Kana rike da lissafin yawan hawayena. Ashe, ba a rubuce suke a littafinka ba?”

Mun kuma isa wajen da akwai mala’iku dayawa. Kodashike a sama mun ga mala’iku daban-daban, amma a nan duka irin su daya ne. Mun ga cewa Yesu ya bada mala’ika wa kowanne mutum, ya kuma gaya mana cewa wannan mala’ikan zai zama kusa da mutum duk tsawon rayuwarsa. Ya gabatar da mu da mala’ikun mu, Ya nuna mana yadda suke amma yace kada mu fada wa kowa. Mun karanta a Zabura 91:11 “Allah zai sa mala’ikunsa su lura da kai, Za su kiyaye ka duk inda za ka tafi”.

Sai muka isa wani wuri mai wasu irin akwati, a cikinsu akwai fure daban-daban. Wasu suna nan a bude da kuma kyaun gani amma wasu sun yi kamar basu sami ruwa ba, wasu kuma sun yankwane. Mun tambayi Yesu menene ma’anar wannan furen? Ya amsa ya ce: “Rayuwar kowanne dayan ku yana nan kamar fure”. Ya dauki fure daya mai kyau sai ya ce: “Wannan yana nuna yanayin zumuntar ka da ni” Ya bar wancan ya dauki wani da ya kasa sai ya ce: “Wannan mutumin ya kasa domin yana chikin lokacin gwaji da kuma wahaloli. Akwai abu a rayuwar wannan da ke shiga tsakanin zumunta na da shi. Ko kun san abinda na ke yi wa furen nan idan sun kasa don in basu lafiya da kuma kyau?” Sai ya dauki furen a hannunsa ya ce “Na kan zuba hawaye na akan su, sai in daga su”. A cikin ikon sa sai muka gan furen ta dawo da rai, ta tashi, ta sami launi masu kyau.

Sai ya dauki yankwanannen furen, ya wurga a wuta, sai ya ce “Duba, wannan mutumin ya san ni amma ya ki ni, baya karbe ni ba har ya mutu an jefa shi a cikin wuta” Yohanna 15:5- 6

Da muka bar wannan wajen, sai muka ga wata kyakkyawar gida chan da nesa. Babu wanda ya isa ya je kusa da wannan gidan, shi ne inda Littafi Mai Tsarki yayi magana game da ita a Ruya ta Yohanna 22:1 “Ya nuna mani kogin ruwa na rai, mai-sheki kamar crystal, yana fitiwa daga cikin kursiyin Allah da na Dan rago”. Mun gaskanta cewa wannan gidan ita ce watakila kursiyin Allah.

Da muke ganin wadannan abubuwan a mulkin sama, muna cike da farin ciki a cikin zukatarmu, muna da salama wadda ta fi dukkan sani (Filibiyawa4:7). Mun gane yadda aka fadi a (I Bitrus 1:4) “zuwa gado mara-rubewa, mara-kazamtuwa, wanda bashi yankwane wa, ajiyayye a sama dominku”.


….(Shaida na shida)….

(Luka 22:30)

“Domin ku ci, ku sha tare da ni cikin mulkina; kuma za ku zamna bisa kursiyai, kuna yin sharia bisa kabilan Israila goma sha biyu”.

A wannan wuri mai ban mamaki, Allah ya yarda mana mu ga kyakkyawar dakin buki da  ba mu taba zata za a samu a duniya ba. Mun ga babban kursiyi da kujeru biyu na zinari da duwatsu masu tamani, wadda babu a duniya. A gaban kursiyin akwai tebiri da bata da iyaka, yana rufe da farar kyalle. Fari ne sal da baza a iya kwatanta shi da kome a duniya ba.

Kowanne irin abinci mai kyau na kan tebirin nan. Mun ga ‘ya’yan itacen inabi masu girmar lemu, Ubangiji Yesu Ya yarda mana mu ci daga cikin su. Har yanzu muna tune da dadin su, abin ban mamaki ne! Dan uwana da abokina, ba za ka iya kwatanta a zuciya abubuwan da Allah ya shirya maka a mulkin sama ba (I Korantiyawa 2: 9)

Akan wannan tebirin kuma, Allah Ya yarda mana mu ga gurasar “Manna”. Wannan ne gurasar Allah wadda Littafi Mai Tsarki ya fadi. An bar mu mu ci daga ciki tare da abubuwan ban mamaki dayawa da babu a duniya.

Duk wadannan abubuwan suna jiran mu ne, gado a mulkin sama. Za mu ji dadin wadannan abincin idan mun gaji mulkin sama. Mun yi mamakin kujerun da ke gefe biyu na teberin, akwai sunaye a rubuce a kan kowanne kujera. Mun karanta sunayen mu a kan kujerun amma sunayen ba wadanda ake kiran mu da su a duniya bane. Sabobin sunaye  ne  wandanda ba wanda ya sani sai mu kadai (Ruya ta Yohanna 2:17). Abinda ke rubuce a Maganar Allah ya ba mu mamaki “Amma domin wannan kada ka yi murna, saboda, ruhohi suna kalkashin ikonku: amma ku yi murna saboda an rubuta sunayenku a cikin sama” (Luka 10:20). Akwai kujeru  dayawa! Akwai kuma isasshen wuri domin duk wadda za su shiga mulkin sama. Akwai wasu kujerun da an dauke daga tebirin. Wannan na nufin akwai maza da matan da sun gaji da bautar Allah, an kuma share sunansu daga littafin-rai, an kore su daga bukin Dan rago.

Allah ya yarda mana mu ga wasu mutane daga Littafi Mai Tsarki, tsarkaka da muke karanta game da su. Mun yi mamakin ganin Ibrahim. Dattijo ne amma ba a jiki ko kamaninsa ba. Dattijo ne a hikima. Sumar sa fari ne gaba daya amma kowanne gashi yana kamar igiyar kwalba ko lu’ulu’u. Abinda yafi ba mu mamaki shi ne mun fi shi tsufa. A sama zamu juya mu zama kamar matasa. Mun yi mamakin kalmomin sa. Ibrahim ya gaya mana abin da ba za mu taba mantawa ba. Ya marabce mu cikin mulkin sama, ya kuma ce mana, a kwanannan za mu zo wannan wajen domin komowar Ubangiji Yesu Kristi ya yi kusa.